🎉💖 BARKA DA SABUWAR SHEKARA, ABOKIYAR RAYUWATA 💖🎉
Sabuwar shekara ta shigo 🕊️, amma ke ce sabuwar farin cikina a kowace rana 🌹.
Zuciyata ba ta san hutu ba idan maganarki ta ambata 💓, domin sunanki yana bugawa tare da numfashina 😍.
Ke ce hasken da ke kore duhun raina ✨,
Ke ce nutsuwata idan duniya ta rikice 🤍,
Ke ce wadda zuciyata ta zaɓa har abada 💍❤️.
A wannan sabuwar shekara 🌙, ina roƙon Allah Ya kare ki, Ya albarkaci soyayyarmu,
Ya cika rayuwarmu da murmushi 😊, fahimta 🤝, da soyayya mara iyaka 💞.
Zan ci gaba da zaɓenki sau dubu 💖,
zan ƙara sonki fiye da jiya 🔥,
kuma zan riƙe hannunki har ƙarshen rayuwa, in shaa Allah 🤲❤️
✍️ Khaleed Khan