Sunday, December 28, 2025

Barka da Safiya kauna

🌞 BARKA DA SAFIYA, KAUNA 🌞
FARIN CIKINA
❣️❣️♥️♥️♥️❣️❣️

Barka da safiya, gaisuwa izuwa gare ki da fatan kin tashi cikin annashuwa da koshin lafiya, abin kauna ♥️.
Safiyar nan ta yi haske, amma hasken zuciyata ya fi kowanne haske saboda kasancewarki a rayuwata.
Jikina yana nan a duniya, amma zuciyata tana tare dake, tana bin ki duk inda kika kasance.

Lokacin da na ji daga gare ki, zuciyata ta cika da natsuwa, kamar iska mai sanyi da ke shafar zuciya.
Babban sirrin da zan iya bayyana wa duniya shi ne: ina kaunarki fiye da yadda kalmomi za su iya bayyana πŸ’ž.
Rayuwata ta haΙ—u da taki, kuma zan rayu tare dake har abada, kamar rana da haskenta da ba za su rabu ba.

I LOVE YOU ❤️

✍️ Khaleed Khan

No comments:

Post a Comment

Barka da Rana, sarauniyata πŸ‘‘ Rana ba ta fara haskawa ba sai da murmushinki ya fara min haske a zuciya ☀️πŸ’ž Ki sani cewa tunaninki shi ne sh...