Ka auri macen daka yadda da ita, ka yadda da nutsuwarta, mutuncinta, tarbiyyarta da addininta.๐ฅฐ
Ka auri wacce zata yi maka biyayya tare da iyayenka ta girmama ra’ayinka sama da nata๐ค
Ka zaษi wacce take sonka da zuciya, ba wai a baki kawai ba.๐๐ป
Ka nemi wacce zata jure zama da kai a lokacin ฦunci ko farin ciki๐ค
Duk mace mai nagarta rayuwarta ta musamman ce: zaka ganta cikin nutsuwa, maganarta nutsuwa, soyayyarta nutsuwa, komai nata daban yake ๐ค๐ฅฐ
Ka auri mace mai girmama manya da yara, wacce tasan hakkin kowa.๐
Ukty Namiji baya son hayaniya. Ki kasance mai nutsuwa da kamala, ki nisanci yawan fushi, ki kasance mai hakuri ๐ค
Maza yanada kyau ku fahimci Akwai lokacin da mace komai nata baya mata daษi musamman lokacin period ko juna biyu. Wannan lokacin zuciyarta tana zafi. Idan kuka fahimci hakan, kar ku zama sanadin zafafa ranta rarrashi takeso๐ฅบ๐
Kema mace, ki sani: Maza da yawa suna fuskantar kalubale a rayuwa a business ko wani abu dabam da zai sa mood dinsu ya canza. Idan bazaki iya zama sanadin rarrashi ba, kar ki zama sanadin ฦara masa damuwa๐
No comments:
Post a Comment