Ka Auri Mace Mai Nagarta 💍✨
Ka auri macen daka yadda da ita, ka yadda da nutsuwarta, mutuncinta, tarbiyyarta da addininta.🥰
Ka auri wacce zata yi maka biyayya tare da iyayenka ta girmama ra’ayinka sama da nata🤍
Ka zaɓi wacce take sonka da zuciya, ba wai a baki kawai ba.👌🏻
Ka nemi wacce zata jure zama da kai a lokacin ƙunci ko farin ciki🤍
Duk mace mai nagarta rayuwarta ta musamman ce: zaka ganta cikin nutsuwa, maganarta nutsuwa, soyayyarta nutsuwa, komai nata daban yake 🤍🥰
Ka auri mace mai girmama manya da yara, wacce tasan hakkin kowa.💕
Ukty Namiji baya son hayaniya. Ki kasance mai nutsuwa da kamala, ki nisanci yawan fushi, ki kasance mai hakuri 🤍
Maza yanada kyau ku fahimci Akwai lokacin da mace komai nata baya mata daɗi musamman lokacin period ko juna biyu. Wannan lokacin zuciyarta tana zafi. Idan kuka fahimci hakan, kar ku zama sanadin zafafa ranta rarrashi takeso🥺💔
Kema mace, ki sani: Maza da yawa suna fuskantar kalubale a rayuwa a business ko wani abu dabam da zai sa mood dinsu ya canza. Idan bazaki iya zama sanadin rarrashi ba, kar ki zama sanadin ƙara masa damuwa💔
Mu kasance farincikin masoyanmu, mu samar wa abokan zamammu nutsuwa da kwanciyar hankali 🤍