🩶 A daren jiya da na yau, wata irin bakuwar kewar ka ta sauka a sansanin zuciyata, ta hautsina dukkan gangar jikina da tsananin tunaninka.
🩶 Na yi mafarkin mu kasance a matsayin ma’aurata, domin da hakan ne da na shayar da kai madarar kauna mai É—anÉ—anon bege da tsagwaran kewar da zuciyata ke É—auke da shi gare ka, sahibina.
🩶 A daren nan, taurari sun yi haske amma haskensu bai kai hasken zuciyata gare ka ba.
🩶 Idan ka kasance kusa da ni, da na lullube ka da zafin soyayya mai ƙona zuciya, da na rungume ka har sai numfashinka ya gauraye da nawa.
🩶 Kewarka ta yi min nauyi, amma soyayyarka ta yi min daɗi fiye da kowanne abu a duniya.
INA KEWAR KA MATUƘA GAYA,
INA SON KA FIYE DA YADDA KALMOMI ZA SU IYA BAYYANA.
No comments:
Post a Comment